Thursday, 17 May 2018

Shugaban 'yansanda yayi ta yin in'ina wajan karanta jawabinshi a gurin wani taro

Wani lamari me ban mamaki cike da abin kunya ya faru da shugaban 'yansandan kasarnan, Ibarim Idris yayin da ya ziyarci jihar Kano dan kaddamar da wani shirin hukumar 'yansandan na leken asiri ranar Litinin din data gabata.


Wani hoton bidiyo daya bayyana a yanar gizo ya nuna Ibrahim Idris yana in'ina wajan karanta jawabinshi a gurin taron inda yayi ta maimaita kalma daya yana abada hakuri akai-akai. 

Wannan lamari dai ya dauki hankulan 'yan Najeriya inda wasu ke ganin cewa hakan abin kunyane wasu kuwa cewa sukayi wai hakan be rasa nasaba da taba Dino Melaye da Bukola Saraji da yayi.

Wasu kuwa sun bayyana hakan da rashin sanin makamar aiki inda suka rika kira da a canjashi.

No comments:

Post a Comment