Tuesday, 22 May 2018

Taurarin kwallo da wasu kewa kallon musulmine: Gaskiyar lamari: na ukunsu zai baka mamaki

Akwai taurarin kwallon kafa da ake rade-radin cewa musulmaine, mutanen da ke dangantasu da musulunci na yin hakane ta hanyar dogara da wasu dalilai da suke gani ko sukaji na cewa 'yan wasan na da alaka da addinin musulunci. To amma menene gaskiyar lamari?.


Dan wasa na farko da masoyanshi da dama ke bayyana shi a matsayin musulmi amma babu tabbacin hakan, shine Ibrahimovic, shidai Movic an haifeshine a garin Malmo na kasar Sweden, mahaifinshi me suna Sefic Ibrahimovic Musulmine kuma yawon ci rani ya kaishi kasar Sweden, mahaifiyarshi me suna Jarka Gravic kuwa Kiristace itama cirani ya kaita kasar Sweden inda ta hadu da mahaifin Zlatan din suka yi aure. Mahaifanshi sun rabu yana dan karamin yaro, bayan rabuwar tasu ya tsaya gurin mahaifinshi amma lokaci zuwa lokaci yakan je gurin mahaifiyarshi, kamar yanda ya taba fadi.

Ya kuma taba fadin cewa kasancewwar mahaifinshi musulmine bazai shafi yanda masoyanshi ke sonshi ba kokuma ya shafi yanda yake buga kwallo ba, domin ita kanta kwallon addinice me zaman kanta.

Wasu kafafe sun ruwaito cewa ya taba bayyana cewa shi kiristane haka kuma wasu sun ruwaito cewa ya taba bayyana cewa shi musulmine amma babu wata sahihiyar kafa ko kuma wata hira da aka taba yi dashi ta rediyo ko ta gidan talabijin ko ta rubutu data tabbatar da cewa shi musulmine.

Tauraron dan kwallo Thierry Henry ya samu daukaka sosai kuma Duniya ta sanshi a shekaru takwas da ya shafe yana bugawa kungiyar Arsenal wasa, dan kasar Faransane kuma yana daya daga cikin wanda suka fi yawan kwallaye a gasar Firimiya ta kasar Ingila dama kasarshi ta Faransa.

Akwai wata magana da Yaren faransanci da Henry ya taba yi akan musulunci wadda ba'a samu ingantacciyar fassara akan wannan maganarba, amma mafi shaharar fassara da ake amfani da ita itace wadda ta bayya cewa, Henry yace yana son abokanshi musulmai sosai kuma yana girmamasu, idan ma akwai wani addini da zai koma to addinin musuluncine.

Wasu sun rika daukar waccan magana da yayi da cewa ya musuluntane.
Robin Van Persie dan kasar Netherlands an haifeshi a yankin Rotterdem na kasar, dan shekaru talatin da hudu, ya haskaka sosai a Duniyar Kwallo inda ya buga wa kungiyoyi irin su Arsenal, Manchester United da sauransu wasa.

Van Persie ya auri 'yar kasar Morocco me suna Bouchra Elbali wadda musulmace, a wata hira da akayi dashi an tambayeshi cewa shin auren musulma yana nufin kaima ka musulunta kenan?, sai ya bayar da amsar cewa, ba gaskiya bane, ni ba musulmi bane, kuma ba kirista bane haka kuma ba bayahude bane, ya kara da cewa ni an reneni a matsayin wanda bashi da addini kuma a haka na taso, idan mutum zai zama munsulmi kamata yayi yayi shi da zuciya daya, bazan musulunta ba wai kawai dan in farantawa matata raiba.

No comments:

Post a Comment