Tuesday, 22 May 2018

'Yan jihar Kwara sunyi gangamin nuna goyon bayan mayar da Kes din 'yan kungiyar asiri da aka kama a jihar zuwa Abuja

Wasu 'yan jihar Kwara, karkashin kungiyar masu kishin jihar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan mayar da kes din 'yan kungiyar asirinnan da ake zargi da kashe wasu mutane a jihar zuwa Abuja. Masu zanga-zangar sunce suna goyon bayan shugaban 'yansanda dari bisa dari akan wannan lamari.


Da yake ganawa da manema labarai jagoran wannan gangami da akayi, yace, sunji dadin yanda hukumar 'yansanda ta mayar da kes din 'yan kungiyar asirin zuwa Abuja saboda irin muhimmancinshi, ya kara da cewa hakan be sabawa doka ba.

Ya kuma ce wannan bashine karin farko da ake mayar da wani kes daga jihar ta Kwara zuwa Abuja ba a shekarun baya akwai kyasa-kyasai da yawa da aka mayar dasu Abuja daga kwarar saboda muhimmancinsu, ciki hadda wanda aka zargi saka Bam a wani kamfanin jarida mallakin Bukola Sataki lokacin yana gwamnan jihar, saboda haka ba sabon abu bane.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kira da ayi adalci wajan yiwa masu laifin shari'a, sun kuma yi kira ga alkalin alkalai na kasa da ya jawo hankalin ma'aikatar shari'a ta jihar da ta daina saka kanta cikin abinda ba huruminta bane.

Hukumar 'yansanda dai ta mayar da binciken wasu daga cikin 'yan kungiyar asiri da aka kama a jihar zuwa Abuja. Dalilin hakan, kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya zargi cewa an mayar da kes din Abujane dan shugaban hukumar 'yansanda ya gogamai kashin kaji. punch.

No comments:

Post a Comment