Friday, 18 May 2018

'Yan kungiyar asiri da aka kama a jihar Kwara da laifin kashe mutane sun bayana cewa gwamnan jihar Abdulfatah Ahmad da kakakin majalisar dattijai Bukola Sarakine ke daukar nauyinsu

'Yan kungiyar asiri da aka kama a jihar Kwara wanda suka amsa cewa sun kashe mutane goma sha daya kuma wasu 'yan siyasane ke daukar nauyinsu, wanda yanzu haka an mayar da Kes dinsu Abuja sun bayyana sunayen gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmad da kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki a matsayin wadanda suke daukar nauyin ayyukansu.


Shafin kwarmato na Sahara Reporters ya bayyana cewa ya samu bayani daga majiya me karfi daga hukumar 'yansandan data tabbatar da wannan labari, shugaban tsagerun wanda dane a gurin wani me magana da yawun magajin garin Ilorin, ya bayyana cewa an saka sunanshi a cikin ma'aikata da ake biya albashi a jihar ta Kwara wanda aka bashi matakin albashi na shashida, sauran abokan aikinshi kuma an basu matakai na goma dana goma sha biyar.

Ya kuma kara da cewa shima kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki yana biyansu Albashi kuma kwanannan ma ya basu motoci kirar Toyoya Corolla a matsayin kamun kafa akan aikin da zasu mishi a zaben shekarar 2019.

Sun kuma kara da cewa yanzu haka suna da mutum biyar da aka basu sunayensu ake so su kashe su kamin zaben shekarar 2019.

Majiya daga hukukar 'yansanda ta tabbatarwa da Shafin Sahara Reporters cewa an samu takardu dake tabbatar da karbar albashi duk wata da masu laifin keyi daga gurin kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki da kuma gwamnan jihar Kwaran Abdulfatah Ahmad, kuma duka masu laifin suna da kudade tsambare a asusun ajiyarsu na banki da suka haura miliyoyin Naira.

Ana tsammanin dai kwanannan hukumar yansandan zata gayyaci Sanata Bukola Sarakin da gwamnan Kwaran, Abdulfatah Ahmad suzo su mata bayani akan wannan lamari. A  Larabar data gabatane dai Bukola Saraki ya fito yayi yekuwar cewa shugaban 'yansandan na shirin bata mishi suna shi da gwamnan jihar Kwaran.

No comments:

Post a Comment