Friday, 25 May 2018

'Yan wasan Madrid sun isa kasar Ukraine

Taurarin kwallon kafar Real Madrid sun isa birnin Kiev na kasar Ukraine inda zasu buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai, a gobe Asabar ne dai za'a buga wasan tsakanin Liverpool da Real Madrid din.A wani labarin kuma magoya bayan kungiyar Liverpool na can ransu a bace bayan da aka soke tafiyar da jirgin da zai kaisu kasar Ukraine din dan kallon wasan duk kuwa da sun biya kudin tafiyar, magoya bayan kungiyar kusan dubu daya abin ya shafa.

Wani me suna Bolland daya shafe shekaru 50 yana goyon bayan Liverpool ya shaidawa manema labarai cewa yayi bakin ciki da bazai je ya kalli wasan ido da ido ba, yanzu saidai yaje gida ya kalla shi da matatshi amma yace babu wata matsala sosai tunda matar tashima masoyiyar Liverpool ce.


No comments:

Post a Comment