Saturday, 19 May 2018

Zaka iya wannan wasa kuwa?: Kalli hotunan gasar Mari da akayi a kasar Rasha

Wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta da ya nuna yanda ake gudanar da wata gasar mari a kasar Rasha, an samu wasu majiya karfine suna gaban mutane kowane na dallawa dan Uwanshi mari iya karfinshi har sai daya daga cikinsu ya gaji ya bada kai.An gudanar da gasar mataki-mataki har aka samu wanda ya zama gwarzo, kuma an bashi kyautar dalar Amurka dari hudu, wannan gasa dai itace irinta ta farko a kasar. Kumatun wadanda suka yi gasar sun kumbura kuma fuskokinsu duk sunyi ja, amma masu kallo sun nuna jin dadin wasan.
Wanda ya lashe gasar yace abin ba sauki, sai mutum ya nuna juriya.
RT

No comments:

Post a Comment