Tuesday, 22 May 2018

Zlatan Ibrahimovic ya samu jan kati bayan da ya fallawa dan wasa mari ana tsaka da kwallo

Tauraron dan kwallo, Zlatan Ibrahimovic ya samu jan kati a wasan da kungiyarshi ta LA Galaxy ta buga da Montreal Impact bayan da ya tallalawa dan wasan Impact me suna Micheal Petrasso Mari.


Petrasso ya takawa Movic kafa shi kuwa sai yayi sauri ya fallamai mari ta baya, dukan 'yan wasan sun fadi a lokaci guda inda kowa ke kokarin samun nasarar Rafli, amma bayan da aka maimaita bidiyon yanda abin ya faru Raflin ya ba Petrasso Katin gargadi shi kuwa Movic aka bashi jan kati na kora.

Duk da haka dai kungiyar LA Galaxy din ce tayi nasara, daci 1-0 a wasan.

Tun bayan da tsohon dan kwallon Juventus, Barcelona da Manchester United din ya koma LA Galaxy kwallaye uku kawai yaci, yadai yi ritaya daga bugawa kasarshi ta Sweden wasa amma kwanannan ya rika neman komawa, kasar dai zata buga gasar cin kofin Duniya ba tare dashi ba.

No comments:

Post a Comment