Wednesday, 13 June 2018

2026: Canada da Amurka da Mexico sun doke Morocco

Kasashen Amurka da Canada da Mexico sun yi nasara a bukatar hadin gwiwa ta neman karbar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya a 2026.


Hadin guiwar kasashen ya doke bukatar Morocco da ke neman karbar bakuncin gasar.

Kasashen sun samu rinjayen kuri'u 136 na mambobin hukumar Fifa, fiye da Morocco wadda ta samu kuri'a 65.

Gasar da za a gudanar a 2026 za ta kasance mafi girma da aka taba gudanarwa, inda kasashe 48 za su fafata a wasanni 80 cikin kwanaki 34.

"Kwallon kafa ta hada kan mu" in ji shugaban hukumar kwallon Amurka Carlos Cordeiro.
"Muna godiya sosai a kan wannan karramawar" a cewarsa bayan tabbatar da nasarar bukatar hadin gwiwar Amurka da Canada da Mexico.

Mambobin Fifa 200 ne suka kada kuri'a daga cikin 211 a taron hukumar karo na 68 da aka gudanar a Moscow a ranar Laraba.

Ana bukatar samun kuri'a 104 ga wadanda suka shigar da bukatar neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

An kebe Amurka da Canada da Mexico da Morocco daga cikin mambobin kasashen da suka kada kuri'a.

Ghana ta kauracewa zaman bayan ta dakatar da hukumar kwallon kafarta saboda badakalar rashawa da ta mamaye kwallon kafa a kasar.

Mexico ta taba karbar bakuncin gasar cin kofin duniya sau biyu a 1970 da 1986.

Haka ma an taba gudanar da gasar cin kofin duniya a Amurka a 1994.

Canada ce ba ta taba karbar bakuncin gasar ba, ko da yake ta karbi bakuncin ta mata da aka gudanar a 2015.
bbchausaNo comments:

Post a Comment