Tuesday, 12 June 2018

Adam A. Zango ya baiwa me Adaidata sahun da ya kamata yaba dari biyar kyautar dubu goma

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya bayyana yanda suna cikin tafiya da mota ta samu matsala, hakan yasa dole suka dauki shatar kekenapep/adaidaita Sahu, Adamu ya kara da cewa rayuwa kenan ba kullun ake kwana a gado ba.


Wani abin kayatarwa shine bayan da me keke Napep din ya kai su Adamun inda zai ajiyesu, suka tambayeshi Nawane kudinshi , ya gayamusu dari biyarne, sai Adamun yace bari ya nunawa Duniya yanda ake karfafa gwiwa, yace a baiwa me kekenapep din dubu Goma.

Adamun ya kara  da cewa ba masu zaman banza ake karfafawa gwiwa ba, masu sana'a akewa:

Adamun ya bayyana hakanne a wani faifan bidiyon daya wallafa a dandalinshi na sada zumunta.

Muna fatan Allah ya saka mai da Alheri.

1 comment:

  1. Allah Biya ka.'Karfafawa mai sana'a gwiwa shi ne abinda ya kamata,domin 'dan zaman banza ya tashi ya nema daga falalar Allah.

    ReplyDelete