Saturday, 30 June 2018

Afirka ta samu koma baya a kwallon kafa>>Drogba

Kwallon kafar Afirka ta samu koma-baya mafi muni cikin shekara 36 bayan fitar da dukkanin kasashen nahiyar tun a zagayen farko a gasar cin kofin duniya , in ji Didier Drogba.


A tarihin gasar kofin duniya, Senegal ta kasance kasa ta farko da aka fitar daga gasar ta hanyar dokar da'a bayan ta sha kashi a hannun Colombia.

Senegal da Japan sun samu maki hudu a rukuninsu amma Senegal ce aka fitar saboda yawan katin gargadi.

Masar da Morocco da Najeriya da kuma Tunisia sun riga sun fice daga gasar a matakin rukuni.

Tsohon dan wasan gaban Ivory Coast Drogba ya ce: "Wata rana Afirka za ta yi nasara, amma muna bukatar sake tunani game da yadda muke tunkarar wadannan manyan gasar."
Babu wata tawagar Afirka da ta taba wucewa matakin kusa da dab da na karshe a gasar kofin duniya.

Yaushe wata tawagar Afirka za ta ci gasar kwallon kafa?
Sai dai kuma, tun shekarar 1982 - a lokacin da Algeria da Kamaru suka fice a matakin rukuni - akalla kasa daya daga nahiyar Afirka tana kai wa zagaye na biyu a gasar. An ci-gaba da hakan zuwa wannan shekarar.

A Rasha, kasashen Afirka sun samu nasara a wasanni uku, amma sun sha kashi a wasanni 10 cikin 15.

Drogba, wanda ya ci kwallo 65 cikin wasanni 104 da ya yi wa Ivory Coast ya kara da cewa: "Wannan babban koma baya ne."

Tsohon dan wasan na Chelsea ya ce yana ganin ganin wata dama ce ga dukkan tawagogin Afirka da kuma hukumar kwallon kafa ta Afirka ta sake dabara kan yadda za a iya ci gaba.
"Mene ne muke son mu yi a gasar kofin duniya mai zuwa? Muna da ikon yin hakan, muna da kudin samun irin wannan cigaban, sai dai muna bukatar fiye da hakan."

"Muna bukatar jajircewa da kuma irin shirin da tawagogin Turai da kudancin nahiyar Amurka suka tanada."

"Wata ranar za mu yi nasara, amma muna bukatar sake tunani game da yadda muke shirya wa irin wadannan manyan gasar." a cewar Drogba.

Kasar Masar ta sha kaye a dukkanin wasanninta a rukunin A da ta buga a Rasha, yayin da Morocco ta samu maki daya kacal a wasanta da Spain a rukuni na B.

Tunisia ta sha kaye a wasanninta biyu na farko a rukunin G kafin ta doke Panama a lokacin da kasashen biyu suka riga suka fice daga gasar, kuma duk da cewa Najeriya ta doke Iceland, ita ma ta fice daga gasar bayan ta karkare a mataki na uku a rukunin D.

Senegal, wadda ta samu zuwa gasar kofin duniya a karo na farko bayan ta kai matakin kusa da dab da na karshe a gasar kofin duniyar da aka yi a shekarar 2002, ta samu maki hudu daga wasanninta biyu na farko a rukunin H bayan ta doke Poland da kuma yin canjaras da Japan.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment