Sunday, 24 June 2018

Ahmad Musa ya zubar da hawaye saboda soyayyar da yaga 'yan Najeriya suka nuna mai

Kwallaye biyun da tauraron dan kwallon Najeriya daga Arewa, Ahmad Musa ya ciwa Super Eagles a wasan da suka buga da kasar Iceland a gasar cin kofin Duniya sun sa 'yan Najeriya da dama kai harma daga wajan kasarnan mutane nata yabamai bisa wannan bajinta da yayi.


A wani gajeren bidiyon da tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad, Sarkin wata ya fitar, yace, ashe dai ana son Najeriyar nan, dan wasa kamar wannan ace ana ajiyeshi a benchi?, ai dalibine ko kuma zaman majlisa ake yi a benchi, wanda ya iya kuwa ko kuma malami, kujera ake girkemai ya rika bada darasi.

Nazir ya kara da cewa, Ahmad Musa yaji dadin yabon da ake ta mishi, yace suma dake kusa dashi sai aika musu da sakon tayashi farin ciki ake sannan saboda murna da yabon da 'yan Najeriya suka rika mishi har saida ya zubar da hawaye.

No comments:

Post a Comment