Friday, 22 June 2018

Ai da ka dawo mana da kasafin kudin tunda baka amince da gyarar da mu kayi ba- Melaye ya fadawa Buhari


Dino Melaye, sanata mai wakiltar kogi ta yamma ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana da damar mayar da kasafin kudin 2018 ga majalisa idan bai gamsu da irin gyaran da su kayi ba.

A ranar Laraba ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin. Sai dai ya ce akwai abubuwan da majalisar su ka kara cikin kasafin kudin da bai gamsu da su ba.

Shugaban kasan ya ce 'yan majalisan sun kara ayyuka guda 6,043 hakan kuma ya kasafin kudin ya karu da naira 14.5 biliyan.

Ya kuma ce sun rage kudaden wasu ayyuka amma dai ya rattaba hannu a kan kasafin kudin ne saboda a fara gudanar da ayyuka a kasar kuma tattalin arzikin ya cigaba da habaka.

A martaninsa, Dino Melaye ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da yunkurin shafawa majalisa kashin kaza a idanun talakawa.

Ya ce dama aikin majalisar shine tattance kasafin kudin da shugaban kasan ya kawo tare da yin gyare-gyare a wuraren da suka dace.

"Fadar shugaban kasa ba ta da ikon dakile ikon da doka ya bawa majalisa. Majalisar bangare ce zaman kanta.

"Idan shugaban kasa bai gamsu da gyare-gyaren da mu kayi ba, yana da damar ya dawo mana da kasafin kudin tare da bayyana wuraren da bai amince da su ba." inji Melaye.

No comments:

Post a Comment