Friday, 29 June 2018

"Al Kur'ani ne babban kalubalen da ya hana kasashen Musulmai ci gaba da kuma wayewa">>Inji jakadan kasar Ausria a Tunisia

Tsohon jakadan Austria a Tunusiya, Gerhard Weinberger ya ce babu ta yadda za a yi a kafa wayayyiyar kasa ta hanyar kafewa da ayoyin Al Kur'ani kawai.


 "Ba za a taba iya gina kasa ba da Kur'ani" , wannan shi ne sunan littafin da tsohon jakadan ya wallafa a gidan buga litattafai na Mymorawa.

A cewar marubucin,"Al Kur'ani ne babban kalubalen da ya hana kasashen Musulmai ci gaba da kuma wayewa. Saboda babu ta yadda za a yi, a gina wayayyiyar kasa ta hanyar kafewa da ayoyin Kur'ani.

A Tunusiya, wadanda suka rungumi rayuwar zamani sun yaki masu bugun gaba da Al Kur'ani da kuma fafutukar ganin an gudanar da komai kamar a zamanin Manzo" in ji shi.

"Yawancin ayoyin Kur'ani sun kafu ne kan wannan tsarin: Duk wanda bai yi imani ba za a hukunta shi...Wannan ba wayewa ba ce ko kuma demokradiyya,kusan sai mu ce kama-karya ce.

Wannan shi babban kalubalen da ke gaban Musulmai.." in ji Weinberger.
Trthausa

No comments:

Post a Comment