Thursday, 14 June 2018

Aladen daya kintatowa Donald Trump nasarar zama shugaban Amurka ya kintatowa Najeriya nasara a gasar cin kofin Duniya

Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya sun cika da murna da farinciki bayan wani alade mai nasibi day a hango nasarar shugaba Trump gabanin zaben kasar Amurka, ya zabi kasashen Najeriya da Argentina nasarar zuwa zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa da za a fara bugawa a kasar Rasha.


Kazalika ya zabi kasashen Belgium da Uruguay a matsayin wasu kasashen da zasu fafata a zagayen kusa da na karshe.

Aladen da ake kira Mystic Marcus na da baiwar sansano duk inda nasara take da hancin sa kuma ya zuwa yanzu bai taba yin kuskure a hango nasara ba.

Mai Aladen, Juliette Stevens, ya bayyana cewar Aladen sa bai taba yin hasashe an samu sabani ba domin ko a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 saida ya hangowa kasar Spain nasara tun kafin a fara gasar.

Wasu abubuwan ban mamaki da aladen ya yi sun hada da has ashen ficewar kasar Ingila daga kungiyar kasashen turai da kuma nasarar shugaba trump a zaben kasar Amurka, a lokacinn da jama’a tuni suka bashi faduwa.

Yanzu abin jira a gani, shine ko hancin Aladen dake sansano nasara ya sansano daidai ko akasin haka a yayin da za a fara buga gasar cin kofin Duniyar ranar juma’a a kasar Rasha.

No comments:

Post a Comment