Wednesday, 27 June 2018

Alkalin wasan daya hura wasan Najeriya da Argentina ya saba dokar FIFA

Alkalin wasan daya hura wasan da aka buga tsakanin Najeriya da Argentina dan kasar Turkiyya, Cunayt Cakir ya aikata babban laifi na karya dokar hukumar kwallon kafa ta FIFA bayan da ya bar dan wasan da jini ke zuba a jikinshi ya ci gaba da buga kwallo.


Wani dan wasan kasar Argentina ya samu rauni a kanshi kuma yana zubar da jini, 'yan kwallon Najeriya sun nunawa alkalin wasan hakan amma sai yayi kunnen uwar shegu dasu.

A dokar FIFA ba'a yarda alkalin wasa ya bar dan wasan da yaji ciwo jikinshi na zubar da jini ba ya ci gaba da buga kwallo a cikin filiba, dole a fitar dashi waje haka kuma ba'a yarda dan wasa ya rika buga kwallo da bandeji da ya baci da jini ba.

Dole sai an duba dan wasa an kuma tabbatar da cewa jini baya zuba a jikinshi sannan alklin wasan ya bashi dama yazo ya ci gaba da buga kwallo.
Foxnews.

No comments:

Post a Comment