Sunday, 10 June 2018

Allah ya kara: Da kai aka dora gwamnatin Buhari: Dan haka duk abinda ya maka daidaine>>Fayose ya gayawa Obasanjo

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi wani bayani dake alamta kamar yana wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Allah kara akan abinda ke faruwa dashi yanzu na bincikenshi da gwamnatin shugaba Buhari yace zata yi.


Fayose yace ai be kamata Obasanjon ya fito yana gayawa 'yan Najeriya cewa wai Buhari na neman tozartashi ba ko kuma zaiyi amfani da shaidun karya ya kamashi ba, kamata yayi ya mika kanshi gurin hukuma dan ya wanke kanshi daga zargin da akemai.

Fayose yace, shine fa Obasanjon da kanshi ya rubuta a littafinshi cewa da Jonathan ya ci gaba da mulki ya lalata Najeriya, gara Buhari ya hau mulki ya kamashi.

Yace kuma be kamata Obasanjon yana korafi akan duk wani abu da Buhari zai mishi ba domin kuwa ya taimaka wajan hawan mulkin na Buhari, sannan matsalar shi kadai ta shaba babu ruwan Yarbawa a ciki.

Yace lokacin da 'yan Najeriya ke dandana kudarsu a mulkin Buhari, Obasanjo yayi ta shiga da fita fadar shugaban kasa yana ta sha'aninshi, haka kuma lokacin da aka kama Sambo Dasuki aka daureshi duk da kotu ta bayar da umarnin sakinshi, da lokacin da sojoji suka kashe 'yan Shi'a a Kaduna, da lokacin da sojoji suka shiga majalisar jihar Eikitin sukayi kame, me yayi, ko kuma me yace?.

Dan haka shima abin ya juyo kanshine yanzu.

Ya kara da kiran shugaba Buhari inda yace, ya sani fa duk abinda mutum yayi shima haka za'a mishi, kuma ba'a dawwama a kujerar mulki.
Thenation.

No comments:

Post a Comment