Monday, 11 June 2018

An kama wani Fasto dumu-dumu yana yayyaga Qur’ani yana konawa a jihar Kogi

Wani Fasto da masu taya shi aiki sun shiga hannu bayan an kama su suna kona takardun Qur’ani mai girma bayan sun yayyaga shi. An kama Faston, da ba a bayyana sunan sa ba, da mukarrabansa dumju-dumu na kona Qur’anin daf da babban masallacin garin Ankpa a jihar Kogi ranar Juma’a, 8 ga watan mayu.

Kona Qur’ani ya fusata wasu matasa har ta kai ga sun ladawa Faston da yaran sa dukan kawo wuka. Saidai, Allah ya takaita da sauran kwanan mutanen a gaba, ‘yan sanda sun zo kafin jama’a su dauki doka a hannun su.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san dalilin Fasto da yaran san a yin hakan ga littafin Qur’ani mai tsarki ba.

No comments:

Post a Comment