Thursday, 14 June 2018

An tabbatar da ganin watan Shawwal a Najeriya

Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya bayyyana Jumu'a, 15 ga watan Yuli a matsayin ranar sallah a Najeriya, bayan ganin watan Shawwal. Wannan shi ya kawo karshen azumin watan Ramadan.


Sarkin musulmin na Najeriya ya ce an ga sabon watan na Shawwal a warare da dama na kasar da suka hada da Sakkwato da Kano da Zaria da Maiduguri da Jos da sauransu.

Hakan na nufin musulmi a Najeriya za su yi bukukuwan Sallah tare da takwarorinsu na Saudiyya da wasu kasashen musulmi da aka sanar da Juma'a a matsayin ranar Sallah.

Tun a ranar Alhamis al'ummar musulmi a jamhuriyyar Nijar suka yi sallah bayan sun riga Najeriya fara daukar azumin Ramadan.

Tuni dai gwamnatin Nigeria ta ayyana Juma'a da Litinin a matsayin ranakun hutu ga ma'aikatan kasar.

Bukukuwan Sallah sun kunshi zuwa Sallar Idi, da saka sabbin tufafi da kuma ziyartar 'yan uwa da abokan arziki.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment