Thursday, 21 June 2018

An Tura Masa Kudin Wasan Sallah Ya Cinye, Kuma Ya Yi Wa Masu Kudin Zagin Kare Dangi

Yadda wani matashin jarumin finafinan Hausa Horo Dan Mama ya zambaci ma'aikatan gidan rediyo na NBS FM dake garin Keffi a jihar Nasarawa. 


Ba a yin rayuwa haka, yau idan kana gwagwarmayar neman duniya ta san ka 'yan jarida na daya daga cikin masu haskaka ka don jama'a su sanka.

Wasu tun duniyar ba ta gama karbar su sai su fara yaudarar kansu wai suna yaudarar mutane, babu dadi yau ka yi wa mutum alkawarin za ka yi masa aiki tun baka fara ba an baka rabin kudin aikin kuma ba ka zo ka yi aikin ba, ka mayar da kudin da aka baka kuma sai cibi ya zama kari.

Wannan yaron babu wanda bai ji labarin cewa zai zo yin wasa a NBS Keffi ba, muka kururuta zuwan sa amma ya saba mana alkawari, kuma ya mayar da kudin da na tura masa ma ya zama tashin hankali. 

Hakan da yayi ya dace da shi? Me kenan ya kamata a kira shi? Shin za ka sake yarda da shi?  

Na kan buga masa waya sau goma bai dauka ba, idan ya dauka sai yace "wanene wannan gaskiya kana damu na". Ka ji fa ni da hakkina. Kai wasu mutanen akan kudi kalilan sai su sayar da mutuncinsu da imaninsu a wurin masoyansu, ka ci kudin idan ka ga dama ka bayar idan baka ga dama ba ka rike kana ci har mahadi ya bayyana.
rariya.

No comments:

Post a Comment