Tuesday, 12 June 2018

Anyi cincirindo domin ganin Gemun Manzon Allah a Turkiyya

A wani babban Masallaci mai dinbin tarihi ne aka fitar da gemun Manzon Allah annabi  Muhammadu (SAW) a lokacin sahuru domin mutane su gani.


A cikin masallacin Ulu dake garin Şanlıurfa an fitar da gemun annabi Muhammadu (SAW) har guda 63 wadanda ake adane dasu tun shekaru aru-aru.

Dubun dubatan mutane sun yi cincirindo domin ganan ma idonsu gemun mai tsarki tare da yin kabbara da salati ga annabi.

An dai bada damar ganin gemun ga mata har izuwa ranar Litini, maza kuwa har izuwa ranar Lahadi.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment