Thursday, 14 June 2018

Anyi Sallar Idi yau a garin Ibadan

Masallacin Idi
Dazu ne mukaji labarin cewa a makwauciyar Najeriya, kasar Nijar anyi bikin Idin Sallah karama wanda mu Najeriya sai yaune za'a fara duban wata, to a Najeriyar ma a jihar Oyo, yau, Alhamis babban limami garin ya jagoranci sallar Idin.

Limamin me suna Sheikh Abdulganiyu Agbotomokekere ya jagoranci sallar inda wasu mabiyanshi suka bishi suka sha ruwa a yau, saidai wasu mazauna garin da dama sun bayyana damuwa da rashin amincewa da abinda limamin yayi inda suka bayyana cewa hakan bai dace ba tun majalisar koli ta harkokin addinin islama da sarkin musulmi basu bayyana cewa anga wata ba, Kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A yaune dai sarkin Musulmi yace Musulmin kasarnan su fara duban jaririn watan Shawwal wanda idan an ganshi to gobe za'ayi bikin sallar idan Allah ya kaimu, in kuma ba'a ganshi ba to sai jibi, Asabar kenan.

No comments:

Post a Comment