Thursday, 28 June 2018

Anyi zage-zage tsakanin 'yan wasan Jamus, me horas dasu da kuma fusatattun 'yan kallo bayan fitar dasu daga gasar cin kofin Duniya

Bayan kammala wasa tsakanin kasar Jamus da koriya ta kudu a jiya a kasar Rasha, wasanda da ya bayar da mamaki ganin cewa kasar Koriya ta kudu na daya daga cikin kasashen da aka bayyana da cewa suna buga wasa mafi muni a gasar amma ta fitar da kasar Jamus me rike da kambun kofin Duniyar, an samu hatsaniya tsakanin 'yan kallo da wasu 'yan wasan Jamus din.


Wasan dai ya kare kasar Koriya ta kudu na cin Jamus 2-0.

Shafin Mirror na kasar UK ya ruwaito cewa a yayin da 'yan wasan kasar Jamus ke kokarin ficewa daga cikin filin wasu gungun 'yan kallo da suke a harzuke da sakamakon wasan sun rika zagin 'yan wasan.

Mesut Ozil yaji ba zai iya jurewa ba shima ya mayar musu da zagin, sai da taimakon jami'an tsaron dake filin sanan suka kama Ozil suka wuce dashi dan kada ya shiga gurin 'yan wasan.

Shima kocin kasar ta Jamus sunyi zage-zage da wasu 'yan kallo da suka sakashi a gaba, shima saida jami'an tsaro suka janye shi.

Anga Ozul cikin fushi ya cire wani damara dake hannunshi ya wurgar da ita saboda haushin fitar dasu da akayi.No comments:

Post a Comment