Thursday, 28 June 2018

Atiku da Obasanjo sun hadu a gurin taro

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya hadu da wanda sukayi aiki tare kuma ake ganin kamar basa shiri, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Abuja gurin wani taro da aka tattauna sabuwar dangantakar Afrika da kasar China.


Kamar yanda me baiwa Atikun shawara akan kafafen yada labarai, Paul Ibe ya wallafa, an ga tsaffin shuwagabannin sun gaisa da juna cikin Raha.

Sauran manyan baki da suka halarci gurin akwai janar Aliyu Gusau me ritaya da tsohon shugaban kasar Benin, Boni Yayi da tsohon shugaban kasar Nijar, Mahamane Ousmane.

No comments:

Post a Comment