Thursday, 28 June 2018

Azumi ne ya hana 'yan wasanmu nasara a gasar kofin duniya>>inji Masar

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Masar ya ce fadowar azumi dab da lokacin gasar kofin duniya ya shafi yadda tawagar kasar ta shirya wa gasar da ake yi a Rasha.


'Yan wasan sun zabi suyi azumi na watan Ramadan duk da lokacin dake tsakanin wasansu na farko da kammala azumin kankani ne.

Kasar Masar, da ta buga da Uruguy da Rasha da kuma Saudiyya, ta fadi a duk wasannin inda ta zo ta karshe a rukuninta ta A.

Abo Rida ya ce 'azumi ya shafi shirinmu na gasar kofin duniya, kuma na yi wa 'yan wasan maganar su ajiye azumin domin shiryawa wa gasar da kyau, amman suka ki suka ci gaba da azumin'.

'Tsakanin wasanmu na farko da Uruguy da kammala azumi rana daya ce ta rabba su, to shi ya sa ba mu yi cikkakken shiri ba'.

Kuma ya kara da cewa 'Ina mai tabbatar muku da cewa kasashen Larabawa da yawa sun sa 'yan wasansu sun sha auzmi'.
Bbchausa.

No comments:

Post a Comment