Saturday, 30 June 2018

Ba na da na sanin rashin aurena>>Tabu

Jarumar fina-finan Indiya Tabu ta ce ba ta da na sanin rashin aurenta ko kadan. Tabu wadda ta fito a cikin fina-finai kamar Maqbool da Chandni Bar da Cheeni Kuma Haider, ta nasar da hakan ne ga wani dan jarida a yayin bikin baje kolin fina-finai da aka yi kasar.
Ko da aka tambayeta shin har yanzu bata yi aure ba, Tabu ta ce kwarai da gaske ita har yanzu budurwa ce.


Jarumar mai kimanini shekara 46 a yanzu, ta ce rashin aurenta ba yin kanta ba ne, lokaci ne bai yi ba, don haka bata da na sanin kasancewarta budurwa.

Kuma idan lokacin auren na ta ya yi, tabbas za ta amarce inji jarumar.

Da aka sake tambayar jarumar ko ta na damuwa da kananan maganganun da wasu mutane ke yi a kan rashin aurenta?

Tabu ta ce ko kadan, domin ita ba ta san ma ana yi ba, don haka ita bai dameta, tunda bayin kanta ba ne.

Kuma zata ci gaba da sanar'arta ta yin fina-finai da sauran harkokin rayuwarta yadda ta saba ba tare da wata damuwa ta rashin aurenta na damunta ba.

Tabu tace ' Idan lokacin da auren na wa yazo, to ko shakka ba bu zanyi shi kuma na zauna kamar kowa, amma tunda yanzu lokacin bai yi ba, zan ci gaba da harkokina kamar yadda na saba ba tare da wata damuwa ba'.

No comments:

Post a Comment