Thursday, 14 June 2018

Ban kai darajar kudin da PSG ta saye ni akai ba>>Neymar

Tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil dake bugawa kungiyar PSG wasa, wanda kuma yafi kowane dan wasa tsada a Duniya, Neymar ya bayyana cewa shifa baya tunanin darajarshi ta kai makudan kudin da PSG din ta fitar ta sayeshi daga Barcelona.


PSG dai ta sayi Neymar a kan kudi sama da Fan miliyan dari biyu daga Barcelona wanda hakan ya dauki hankulan Duniya sosai, Neymar ya fara taka rawar gani a PSG din amma ciwon da yaji ya kawomai cikas.

Da yake magana da kafar watsa labari ta Express anji Neymar din na cewa, Shifa kudin da aka sayeshi akai basa sashi yaji cewa shi wanine, kudi ne kawai, baza su sashi yaji girman kaiba, da ace shine bazai taba sawa kanshi wadannan zunzurutun kudinba.

No comments:

Post a Comment