Monday, 11 June 2018

Ban so Madrid suka ci kofin zakarun turai ba>>Messi

Tauraron kwallon kafar Barcelona, Lionel Messi ya bayyana irin yanda ya kalli wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai wanda aka buga tsakanin Real Madrid da Liverpool a birnin Kiev na kasar Ukraine, wasan ya kare inda Madrid ta lallasa Liverpool din daci 3-1, Messi yace beji dadin nasarar da Madrid din ta samu ba.


ExpressUK ta ruwaito cewa, manema labarai sunyi hira da messin wanda yanzu haka tawagar kasarsu, Argentina sun isa kasar Rasha inda zasu buga gasar cin kofin Duniya, shin ya kalli wasan karshe din tsakanin Liverpool da Madrid?

Sai yace ya fara kalla amma be gama ba, yaso ace ya kalla amma saboda ba lokaci shiyasa be samu dama ba, ya kara da cewa tunda aka ciresu daga gasar,sai ya tafi kasarshi Argentina dan shiryawa gasar cin kofin Duniya.

Yace amma ya kalla maimaicin wasan daga baya.

Ya kara da cewa, shi yana so yayi nasara ne a karan kanshi, abinda sauran kungiyoyi sukeyi be dameshi ba. Yace, a  matsayina na dan kwallon Barcelona, idan aka fitar damu daga wata gasa to bazanso babbar abokiyar hamayyarmu tayi nasaraba.


No comments:

Post a Comment