Monday, 11 June 2018

Bana tsoron Suarez saboda nima na iya cizo: Salah kuma irin abinda Ramos yamai zan mai>>Inji dan wasan baya na kasar Rasha Kutepov

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kasar Rasha, Ilya Kutepov ya bayyana cewa baya jin tsoron 'yan wasa irin su Mohammed Salah da Luis Suarez, kasar ta Rasha tana aji na A ne wanda ya kunshi kasashen Uruguay, Saudi Arabia da Egypt.Da yake magana da manema labarai,  bayan wasan sada zumunta da suka buga da kasar Turkiyya, Kutepov ya bayyana cewa, bana jin tsoron Suarez, idan ta kama ni da kaina zan fara cizonshi, kamin ya cijeni.

Ya kara da cewa, Salah ma ba wata matsala bane, Ramos ya nuna mana yanda ake maganinshi, zan iyamai abinda Ramos yamai.
Marca

No comments:

Post a Comment