Saturday, 30 June 2018

Bayan halatta musu tukin mota, kasar Saudiyya ta kuma halattawa matan kasar tuka babur

Bayan izinin tuka mota,shugabannin Saudiyya karkashin jagorancin Muhammad bin Salman sun wuce mataki na gaba,watau hallata wa mata hawa babura.


Iskar juya juyin hali na ci gaba da kadawa a Saudiyya,tun a lokacin da yarima mai jiran gado,Muhammad bin Salman ya karbi akalar mulkin kasar.

A watannin da suka gaba, yarima bin Salman ya bai wa mata kasarsa izinin tuka mota,inda a yanzu kuma ya hallata musu hawa babura.

An tabbatar da cewa,a yanzu haka matan Saudiyya na ci gaba da cincirindo don zuwa cibiyoyin koyon tuka babura.

Yadda lamurra ke ci gaba da sauyawa a Saudiyya babu kakkautawa, na ci gaba da tayar da hankulan Musulman duniya,musamman ma 'yan Sunni,wadanda tun fil azal suke yi wa masarautar kallon abar kwantace.
Trthausa

No comments:

Post a Comment