Thursday, 28 June 2018

Baza mu sake zuwa aikin hajji ba>>Limaman kasar Tunusiya

Manyan limaman kasar Tunusiya sunyi kira ga Muftin kasarsu daya yi kokarin ‘yantar da jama’arsu daga aikin hajji, ganin yanda farashin kujerun zuwa kasar Saudiyyan ke ta faman karuwa, sannan kuma sunyi ikirarin cewa kasar ta Saudiyya tana amfani da kudin musulmai masu zuwa aikin hajji wurin yakar al’ummar musulman duniya


Gidan rediyon Shems dake kasar Tunusiya sune suka rawaito wannan labari, inda suka ce sakatare janar na kungiyar manyan limaman kasar, El Fadel Ashur ya kira Muftin kasar ta Tunusiya da murya mai karfi akan ya fitar da fatawar da zata saka musulman kasar su daina zuwa aikin hajji.

A yanda limaman suka fada a shafin watsa labarai na ‘Algerie Focus’, sun bayyana cewar a ‘yan shekarun nan farashin kujerun aikin hajji sunyi tsada sosai, sannan kuma irin dumbin kudaden da kasar Saudiyya take tarawa, tana amfani dasu ne wuin yakar al’ummar musulman duniya.

No comments:

Post a Comment