Monday, 11 June 2018

Chelsea na fuskantar barazanar sayarwa, har an taya €21b

Biyo bayan rashin tabbas ga makomar mamallakin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Chelsea ɗan asalin kasar Rasha Roman Abramovich a ƙasar Ingila, yanzu haka shahararren mai kuɗin nan na ƙasar ta Ingila Jim Ratcliffe ya taya Chelsea zunzurutun kuɗi har £21b.


Tun dai hawan sabuwar Firaministar ƙasar Theresa May dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu, wanda hakan ke barazanar cigaba da zaman Abramovich ɗin cikin Ingilan sakamakon wahalar sabunta Fasfo ɗinsa.

An dai rawaito cewa mamallakin Chelsea ya hasala matuƙa bisa hana shi shiga kallon wasan ƙarshe na cin kofin FA da Chelsea ta buga ranar 19 ga watan Mayu inda daga bisa cikin kwanaki ƙalilan ya nemi takardar zama ɗan ƙasar Isra'ila kuma aka ba shi ba tare da ja'in ja ba.

Matuƙar dai ba'a sabuntawa Abramovich Fasfon na shi ba, to ba zai samu damar gudanar aiki a ƙasar ba duk kuwa da cewa yana da damar shigowa ƙasar har na tsawon watanni shida ta hanyar amfani da sabon Fasfon da Isra'ila ta bashi.

An dai ƙiyasta darajar kuɗin mai shirin siyan Chelsea zai kai har £45bn kamar yadda yazo na ɗaya a jadawalin Sunday Times. Yana da mutane 18,500 a ƙasashen 22 da suke masa aiki.

Shi dai Mr Ratcliffe magoyin bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ne sosai domin har gida yake da shi a kusa da filin wasa na ƙungiyar. Sai dai kuma wasu rahotannin sun bayyana cewa Abramovich ɗin ya ƙi amincewa da tayin, domin a shirye yake da ya cigaba da riƙe ƙungiyar.

Abramovich ya sayi ƙungiyar ta Chelsea ne a shekara ta 2003 kan kuɗi £140m.


No comments:

Post a Comment