Thursday, 21 June 2018

Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015>>Inji PDP

Da kudin barayi Buhari yaci zaben 2015 - Inji PDP
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bayyana cewa shugaban kasar Najeriya baya da wata kima ko kwarjinin da zai zo yana ta faffaka game da yaki da cin hanci da rashawa idan dai har bai binciki inda kudaden kamfe din sa na 2015 suka fito ba.


Wannan kalamin dai sun fito ne daga ofishin babban sakataren yada labarai na jam'iyyar ta PDP Kola Olagbondiyan a yayin wani taron jam'iyyar a jihar Kogi.

Mista Kola ya ce abun takaici ne yadda shugaban ke fitowa yana ta kumfan baki game da yaki da cin hanci da rashawa amma kuma a dayan bagaren yana zagaye da barayi.


No comments:

Post a Comment