Saturday, 2 June 2018

Dattijo Dan Shekaru Fiye Da Dari Da Ya Yi Ikrarin Cewa Ko A Baro Zai Je Rumfar Zabe Don Ya Sake Zaben Buhari A 2019 Ya Rasu

Wannan wani bawan Allah ne da jaridar Rariya ta taba yin hira dashi wanda saboda soyayyarshi ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gaya musu cewa ko a baro za'a kaishi sai ya sake zabar Buhari, Allah ya mai rasuwa.


Ga yanda jaridar ta Rariya ta bayar da labarin kamar haka:

Innalilahi wa inna ilaihi raji'un.

Ko Za ku Iya Tuna Wani Tsoho Mai Kimanin Shekaru Fiye Da Dari Wanda Yake Zaune Cikin Karamar Birnin Dake Jihar Kano, Wanda Ya yi hira Da Jaridar RARIYA Ranar 07/08/2016 Inda Ya Bayyana Cewa " Ko A Baro Zai je Rumfar Zabe Domin Sake Jefawa Buhari Kuri'a A Zaben 2019"

Tsohon Mai Suna Malam Suleman Auwal Mai Kimanin Shekaru Fiye Dari Wanda Yake Zaune A Cikin Karamar Hukumar Birni Dake Jihar Kano, Allah Ya yi Masa Rasuwa Yau Kimanin Watanni Uku. 

Yayin  Da Jaridar RARIYA Take hira Da Marigayi Malam Suleman Auwal, Ya Bayyana Cewa Shi Yana Siyasa Ne, Saboda Buhari Kuma Muddin Yana Raye A Zaben 2019 Ko Akan Baro Zai je Rumfar Za6e Domin Jefa Buhari Kuri'arshi. 

Sai Dai Allah Bai Bashi Damar Ganin Wannan Lokaci ba. 

A madadin Jaridar RARIYA Muna Mika Sakon Ta'aziyya Ga 'Yan Unwasa Tare Da Addu'ar Allah Ya Jikanshi Da Rahama Amin.

 Sai Dai Tsohon Ya Rasu Ya bar Mata Daya Da 'Ya Daya, Wanda Gaskiya Suna Bukatar Agaji.

No comments:

Post a Comment