Sunday, 10 June 2018

Dawa-dawa ka shirya ba barka da Sallah?

Nan da ranar Juma'a ko Asabar idan Allah ya kaimu za'ayi Idin Sallah karama, bayan Ibada da zumunci da ake sadarwa a lokacin bukukuwan sallar, wani abu dake zukatan mutane, musamman matasa shine kyautar barka da Sallah.


Ana bayar da abubuwa daban-daban a matsayin kyautar barka da Sallah amma kayautar da ta fi shara kuma mutane suka fi so ita ce ta sabbin kudi.

Saurayi na baiwa budurwarshi barka da Sallah.
Miji yana baiwa mata.
Wa yana ba kannenshi.
Iyaye suna baiwa 'ya'ya.
Masu kudi, musamman 'yan siyasa suna baiwa marasa karfi.
Da kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Shin a wannan Sallar dawa-dawa ka shirya baiwa barka da sallah?
Ko kuma wa kake tsammanin zai baka barka da Sallah?.
Fadi sunanshi dan ka tuna mishi yayi tanadi.

Allah ya sa ayi bukukuwan Sallah lafiya ya kuma amsa mana Ibadunmu.
Hoto: Daga A'ishatulhumaira.

No comments:

Post a Comment