Thursday, 21 June 2018

Duk da kwallayen da Ronaldo yaci: Kasar Iran tayi abinda yafi daukar hankali a gasar cin kofin Duniya

Wani jifan kwallon da dan wasan baya na kasar Iran Milad Mohammadi, ya so ya yi ya shafe duk wani abin bajinta da aka yi a wasannin da aka buga na cin kofin kwallon duniya a ranar Larabar data wuce.


Wannan jifa da dan wasan ya yi a cikin mintin karshe na wasan da Spain ta doke Iran, ya haifar da muhawara da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da kuma bakunan masu sharhi kan wasan kwallon kafa.

Abin ya faru ne a dai-dai lokacin da ake gab da tashi a wasan, sa'ilin da Iran ke matukar bukatar jefa kwallo guda daya domin yin canjaras da Spaniya.

Milad Mohammadi, ya dauki kwallon bayan da ta tsallake layi domin yin jifan turoyin.
Ya ja da baya sosai, ya sumbaci kwallon da ke hannunsa, sannan ya rugo da gudu ba tare da ya jefa kwallon ba.

Daga nan ne ya sake ja da baya, a yayin da ya rage saura dakika talatin a tashi wasa, ya sake sumbatar kwallon ya taho da gudu ya yi alkafura a kasa sannan ya mike tsaye a dai-dai bakin farin layi da niyyar jefa kwallon zuwa cikin fili, inda sauran 'yan wasa ke jira.

Sai dai alkalin wasa ya katse masa hanzari ta hanyar hura usur, sannan ya bukace shi da ya jefa kwallon kamar yadda aka saba yi.

Wannan al'amari dai ya bai wa masharhanta da kuma masu kallo mamaki, abin da ya sanya hakan ya zama babban labari jim kadan bayan kammala wasan.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment