Thursday, 28 June 2018

FIFA ta hukunta Maradona saboda zagin da yawa 'Yan Najeriya

Saboda yanda yayi murnar nasarar da kasarshi ta Argentina ta samu akan Najeriya ta hanyar zagin magoya bayan Super Eagles, hukumar kwallon kafa ta FIFA ta hukunta Diego Maradona.


Bayan da Rojo yaci Najeriya kwallo ta biyu, Maradona ya tashi ya daga hannu yayi alamar zagi da kuma fadin zagin da bakinshi ga masoyan Super Eagles dan nuna murnarshi akan nasarar da Argentinan ta samu.

Hakan yasa FIFA tace, ta daina biyanshi kudin wakilcin da yake mata da suka kai Yuro dubu goma, sanan kuma ta gargadeshi akan kada ya sake yin irin wannan abu idan ba haka ba za'a hanashi shiga kallon wasan kasar tashi ta Argentina, kamar yanda Owngoal suka ruwaito.

Koda likitan Maradona sai da ya gargadeshi da kada ya kalli wasan kasar da Najeriya dan kare lafiyarshi amma yayi taurin kai yaje, ai kuwa da aka kammala wasan saida likita ya dubashi saboda jinishi ya hau.

No comments:

Post a Comment