Monday, 11 June 2018

Gidajan talabijin 8 na kasar Morocco suka nuna saukar shugaba Buhari kasar kai tsaye

Ziyarar shugaba Buhari a kasar Morocco na ta kara daukar hankulan mutane musamman a Najeriya, lura da irin tarbar karamcin da aka mishi, rahotanni sun bayyana cewa gidajen talabijin takwasne suka nuna isar shugaba Buhari kasar, kai tsaye.Me baiwa shugaba Buhari shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka.

Hakan na nuna yanda suka dauki ziyarar ta shugaba Buhari da muhimmanci.

No comments:

Post a Comment