Friday, 29 June 2018

Gidan jaridar Premium Times ya nemi afuwar Miyetti Allah bisa labarin da suka buga akan kuskure na cewa kungiyar ramuwar gayya tayi akan kisan Filato

A makonnanne aka samu wani rahoto dake cewa shugaban Miyetti Allah yankin Arewa maso tsakiya Danladi Ciroma ya kare kisan da ake zargin fulani makiyaya dayi na ramuwar gayya a jihar Filato da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama inda aka ruwaito cewa Danladin yace ramuwar gayyace sukayi saboda shanunsu da aka sace musu.


Bayan da gidanjen jaridu da dama suka watsa wannan labari, Danladi Ciroma ya fito ya karyata cewa shi bai fadi waccan magana ba kazafi aka mishi.

Gidan jaridar Premium Times ya zama gidan jarida daya tilo da ya fito ya bayar da hakuri akan wannan labari da ya wallafa inda yace me aika musu da rahotone daga jihar Filato ya yaudaresu har suka wallafa wannan labari da tunanin cewa tabbas Ciromane yayi wannan magana.

Gadai abinda gidan jaridar yace:

A bincike da muka gudanar game da haka ashe wani dan jarida ne ya kissa wannan magana cewa wai shi Ciroma ya fadi haka inda ya aika wa ‘yan uwansa manema labarai ta shafin guruf din su a WhatsApp.

Daga nan kuma sai suka yada ta ganin cewa shi wannan dan uwa nasu dan jarida ne ya tabbatar musu da samun wannan magana na Ciroma baki-da-baki.

Amma sai dai bayan binciken da aka gudanar, sai aka gane cewa tabbas, akwai gashi a cikin maganar, aka gano cewa Ciroma bai taba yin irin wannan magana ba.

A haka dai har da mu Jaridar PREMIUM TIMEs sashen mu na turanci da muka dauki labarin kuma muka gudanar da binciken muke janye wannan magana sannan muke rokon yafiya ga kungiyar Miyetti saboda mamayar mu da akayi a kai har muka fada irin haka bayan ashe shi kan shi wakilin mu ya shammace mu ne cewa da shi aka yi magana baki-da-baki bayan ba haka bane shima dauka yayi a jaridar Nation.

No comments:

Post a Comment