Saturday, 9 June 2018

Gobe Shugaba Buhari zaikai ziyara kasar Morocco

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zaikai ziyara kasar Morocco gobe, lahadi Idan Allah ya kaimu, shugaban zai gana da sarki Muhammad VI kuma zasu tattauna batutuwan da suka shafi cigaban kasashen biyu.


Me magana da yawun shugaba Buhari a wata sanarwa daya fitar ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da zasu tattauna hadda maganar samar da taki ga manoman Najeriya batun da tun ziyarar da Sarki Muhammad VI ya kawo Najeriya a shekarar 2016 aka farashi.

Gwamnonin jihohin Jigawa da Ebonyi ne tare da wasu manyan jami'an gwamnati zasu yiwa shugaba Buhari rakiya.

Muna fatan Allh ya kaishi lafiya ya kuma dawo dashi lafiya.

No comments:

Post a Comment