Monday, 11 June 2018

Gwamnati Ta Bayyana Ranakun Hutun Bukukuwan Sallah

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun 15 da 18 ga wannan wata na Yuni a matsayin ranakun hutun bukukuwan sallah.


Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurahman Danbazau ne ya bayyana haka inda ya nemi al'ummar Nijeriya su yi amfani da wannan dama na yi wa Nijeriya Addu'o'in samun zaman lafiya, hadin kai da kuma ci gaba. 

Haka ma, Ministan ya nemi Musulmi su yi amfani da darussan da suka koyi a lokacin Azumi wajen gudanar da rayuwar sadaukarwa da jin kan juna tare da bayar da hadin kai ga gwamnatin Buhari wajen ciyar da kasar nan gaba.

No comments:

Post a Comment