Saturday, 9 June 2018

Gwamnati Za Ta Sake Waiwayar Batun Kisan Bola Ige Wanda Obasonjo Ke Da Hannu A Ciki

Jaridar ' Leadership' ta ruwaito wata majiyar rundunar 'yan sanda wadda ta nuna cewa gwamnati ta kammala duk wasu shirye shirye na sake bude bincike kan kisan Tsohon Ministan Shari'a, Bola Ige a shekarar 2003 wanda ake zargin Olusegun Obasonjo da hannu cikin kisan.


Majiyar ta nuna cewa duk da yake a wancan lokacin kotu ta wanke wanda ake zargi da kisan, Iyiola Omisore amma doka ya bayar da dama na sake ci gaba da bincike kan laifin. Haka ma, rundunar 'yan sandan za ta sake bude bincike kan kisan da aka yi wa jigon Tsohuwar jam'iyyar ANPP, Marshall Harry, a zamanin mulkin Obasonjo.

No comments:

Post a Comment