Friday, 29 June 2018

Gwamnatin tarayya ta ware biliyan 10 dan talkafawa wadanda rikicin manoma da makiyaya ya shafa

An jima ana samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohin Benue, Nasara da Plateau, rikicin da yayi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyin al-umma, gwamnati na daukar matakai dan ganin ta shawo kan wannan lamari, daya daga cikin hanyar da gwamnatin tarayya ta dauka dan shawo kan wannan lamari shine gonakin da aka lalata sanadin wannan rikici.


Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Muhammad Buhari ya amince a ware Naira Bilyan 10 don gyaran gonakin da rikicin makiyaya da manoma ya janyo lalacewarsu a jihohin Binuwai, Nasarawa da Filato tare kuma da tallafawa al'ummomin da rikicin ya shafa.

No comments:

Post a Comment