Sunday, 24 June 2018

Haramcin tuki ga mata ya kawo karshe a Saudiyya

Mata a Saudiyya a yanzu suna da 'yancin tukin mota bayan wa'adin haramcin yin haka ya kawo karshe a ranar Lahadi. A watan Satumba ne gwamnatin Saudiyya ta sanar da dage haramcin tuki ga mata, kuma tuni aka fara ba matan lasisin tuki a Saudiyya.


Kafin dage haramcin Saudiyya ta kasance kasa ta karshe a duniya da mata ba su da izinin tuki.

Sai dai duk da wannan ci gaban ga matan Saudiyya, ana zargin hukumomin kasar da bin matakai na murkushe wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da ba mata 'yancin tuki a kasar.

Kungiyar Amnesty International da ke rajin kare hakkin dan adam ta ce akalla mata 'yan gwagwarmaya takwas aka kama, kuma za su iya fuskantar shari'a a kotun yaki da ta'addanci tare da fuskantar hukunci mai tsauri.

Amnesty ta bukaci Saudiyya ta kara tabbatar da wasu sabbin sauye-sauye musamman ga lamurran da suka shafi 'yancin mata.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna gwagwarmaya domin ganin Saudiyya ta ba mata 'yancin tuki a kasar.

An kame mata da dama saboda tuki a Riyadh a 1990, yayin da wasu mata suka dinga wallafa bidiyonsu a kan sitiyarin mota a 2008 da kuma tsakanin 2011 da 2014.

Sai dai kuma wasu mazan Saudiyya da dama sun bayyana rashin jin dadi da sabon sauyin da aka samu, inda suke amfani da maudu'i a intanet da ke cewa "Ba za ku yi tuki ba"

Dage haramcin tukin ga mata na daga cikin sabbin manufofin Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman na kokarin bunkasa wasu fannonin rayuwa a Saudiyya.

Matakin na daga cikin shirinsa na shekara ta 2030 da nufin karkatar da tattalin arzikin Saudiyya daga dogaro da arzikin man fetir zuwa nishadi da yawon bude ido.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment