Monday, 11 June 2018

Hoton Donald Trump shuwagabannin kasashe na zagaye dashi ya dauki hankula: Wai suna koya mai binda zaiyi ne

A gurin taron kungiyar kasashen Duniya bakwai masu karfin tattalin arziki da akayi, an dauki wannan hoton na shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana zaune, yayin da sauran shuwagabannin kasashen Duniya ke tsaye a gabanshi, shugabar Jamus Agila Markel ta dafa teburi tana kallonshi, yana yin hoton ya dauki hankulan mutanen.


Jama'ar kasar Amurka da dama sun bayyana hoton da cewa kamar sauran shuwagabannin suna koyawa Trump yanda ake huldar diplomasiyya da kasashen Duniyane, irin be san a binda ya kamata yayi din nan ba, an rika rubuta magan-ganun barkwanci akan hoton da kuma canja mishi yanayi.

Masu yiwa Shugabar Jamus hidima ne suka dauki hoton kuma suka wallafashi a shafinsu na sada zumunta tun daga nan sai ya fara yaduwa kamar wutar daji. Trump dai ya roki a dawo da kasar Rasha cikin kungiyar kasashen dake da karfin tattalin arzikin abinda sauran kasashen suka ki yarda dashi. Shuwagabannin kasashen da suka halarci wannan taro sun hada da na kasar Italiya, Kyanada, Uk, USA, Japan, Jamus da kuma Faransa.

Ga wasu yanda aka canja hoton:No comments:

Post a Comment