Sunday, 10 June 2018

Hukumar JAMB ta samar da kudin shiga mafi yawa a tarihinta

A zamanin shuwagabannin baya, kamin zuwan shugaban kasa, Muhammadu Buhari hukumar shirya jarabawar share fagen shigaba Jami'a JAMB tana samar da kudin shiga kimanin miliyan hamsin da biyu amma karkashin gwamnatin shugaba Buhari hukumar ta JAMB ta samar da kudin shiga biliyan tara a shekara daya.


Me baiwa shugaban kasa Shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad da kuma me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu suka bayyana haka. Daga biliyan tara da JAMB din ta samar, ta saka biliyan bakwai da miliyan dari takwas asusun baitilmain gwamnatin tarayya.

No comments:

Post a Comment