Saturday, 2 June 2018

Ina tausaya wa masu kokarin kare gwamnati ta daga masu adawa>>Buhari

A ranar juma'a ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna tausayawar shi ga masu kare shi da Gwamnatin shi, yace ba abu ne mai sauki ba, kare gwamnatin shi a gurin 'yan adawa.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda SGF, Mista Boss Mustapha (61) da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Malam Abba kyari, a wata tataunawa da shugaban kasan ya ba yan kungiyar watsa labarai ta Buhari, inda Mista Austin Buraimoh ya jagorance su a gidan gwamnati, a Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a lokacin da ya karbi yan kungiyar a fadarshi dake Abuja. Shugaban ya nuna tsoron shi akan rashin hali da jam'iyyar adawa take dashi, wanda zai hana su iya fito na fito da APC.

Yayi godiya ga kungiyar sakamakon sadaukarwarsu. Har ma ya tausaya musu na rashin abokanai da sukayi sakamakon tallafa mishi da suke ba tare da samun wata riba ta kudi ba.

Kungiyar dai ta yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ce tun 2015.

No comments:

Post a Comment