Thursday, 21 June 2018

Iran ta haramta wa 'yan kasarta kallon wasan da ta buga da Spain

Iran ta haramta wa 'yan kasarta kallon wasan da ta buga da Spain,inda ta bada umarnin yada bidiyo da kuma hotunan galabar da ta yi kan Morocco.A cewar shafin yada labarai na Entekhab da ke Iran, a daidai karfe  goma na yamma a gogon kasar,'yan sandan yankin Meshed sun fitar da wata rubutacciyar sanarwa da zummar rufe gidajen shan kofi,inda a nan  ne jama'a ke taruwa don kallon kwallo .

An sanar da cewa an dauki wannan  matakin dakiku 30 kafin kungiyar kwallon kafar kasar ta kara da ta Spain a gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018.

Amma an bada damar yada hotuna da kuma bidiyon murna da annashuwar Iraniyawa bayan da galabar da kasarsu ta yi kan Morocco (ci 2 da 1) a ranar Jumma'ar nan da ta gabata, a kafafan sada zumunta da na yada labarai.

Kasar Spain dai ta lallasa Iran da ci 1 da nema.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment