Friday, 29 June 2018

Jamhuriyar Asgardia, kasa ta farko ta sararin samaniya

Wani hamshakin attajirin Rasha ya kafa jamhuriyar Asgardia,kasa ta farko ta sararin samaniya.


Jaridar Newsweek ta Amurka wacce ta rawaito labarin, ta ce an gudanar da bikin kafa wannan sabuwar kasar, a ranar 25 ga watan Yunin bana, a fadar Hofburg da ke a Vienna, babban birnin Austria.

Yayin da yake magana gaban manema labarai, hamshakin Barashen,Igor Ashurbeyli ya ce,

"Mun kafa jamhuriyar Asgardia, kasa ta farko ta sararin samaniya.Nan da wani matsakaicin zamani, za a fara gina muhallan Asgardiyawa da kuma kafa wasu katafarun birane a duniyar wata.".

An tabbatar da cewa, kafa Asgardia ke da wuya,kusan mutane dubu 200,000 ne suka nemi shaidar zama 'yan kasar.

A yanzu haka Asgardia ta tanadi, tuta,take,fasfo,'yan majalisu, shugaba,ministoci,kundin tsarin mulki,bankuna,intanet da ma duk wani abu da kowace wayayyar kasa ke bukata.

A shekarar 2016 ce, a karo na farko biliyoniya Ashurbeyli ya dauki alkawarin kafa jamhuriyar Asgardia,inda ya ce,

"Kafuwar wannan kasar, wani sabon cigaba ne a wayewar bil adama".
Trthausa.

No comments:

Post a Comment