Friday, 29 June 2018

Jarumin Bollywood Suniel Shetty ya koma waka

Jarumin fina-finan kasar Indiya, Suniel Shetty, da aka jima ba aji duriyarsa ba a fina-finai, yanzu zai fara waka bayan shafe shekara 18 rabonsa da wakar.


Suniel Shetty ya ce, yana matukar kewar magoya bayansa, hakan ya sa ya yanke shawarar ba ri ya taba waka, amma ta cikin fina-finai ba.

Mutane da dama dai ba su san jarumin ya taba yin waka a shekarar 2000 tare da wasu yara inda aka sawa wakar suna 'Jantar Mantar'.

Rahotanni sun ce, yanzu jarumin ya rera wata 'yar takaitacciyar wakar bidiyo amma tallan wata tashar rediyo ce wakar.

Suniel Shetty, ya ce ya yi wa tashar rediyon wadda ba a budeta ba tukunna waka ne don ya dawo da basirarsa ta waka.

Jarumin ya ce, saboda jimawar da ya yi bai yi waka ba, sai da ya yi ta gwaji kafin a dauki wakar.

Suniel Shetty, ya ce, duk da muryarsa ba ta dadi a wajen fitar da sautin waka, shi mai sha'awar wakar ne.

Koda aka tambayeshi ko ya taba waka a cikin fina-finan Indiya, jarumin sai ya yi dariya, sannan ya ce " Bai taba yi ba, amma kuma idan har magoya bayansa suna bukatar ya rinka waka a cikin fina-finan kasar, to zai gwada".

Jarumin ya ce, ya samu kwarin gwiwar yin waka ga sabuwar tashar rediyon ne, saboda goyon bayan da ya samu daga iyalansa.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment