Sunday, 10 June 2018

'Ka Yi Murabus, Ba Nasara A Tare Da Kai!' Sheikh Gumi Ya Gargadi Buhari

Image may contain: 1 person
Babban shehin malamin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce da Buhari ya yi Murabus saboda kashe-kashen da ake a karkashin shugabancinsa. Yayin gabatar da Tafsirin Al-Qur'ani mai girma na wannan azumin, shehin malamin ya soki gwamnatin Shugaba Buhari kan abubuwa da dama, tare da kamantata da tsohuwar gwamnatin Shugaba Jonathan.


Domin karfafa hujjarsa, Sheik Gumi ya nuna wani fejin farko na jaridar 'New Nigerian' inda yake sukan Jonathan tare da gargadinsa kan lallai ya yi Murabus a lokacin da ana tsaka da rikicin Boko Haram.
Malamin yake cewa: "Dalilin da ya sa na daura alhakin jinin al'umma da ya zuba a wuyan Jonathan shi ne, 'yan Boko Haram sun ta dasa bama-bamai a ko'ina amma ba wani abin kirki da gwamnatin ta dinga yi.

"Kai ke da alhakin jinin duk wanda aka kashe yayin shugabancinka. Idan ka yi bakin kokarin ka, zan iya cewa eh, Allah zai iya yafe maka. Amma idan bakai komai ba, a'a; Allah ba zai yafe maka ba. Don haka a yanzun ma haka ne.

"Zubar da jinin da ake a yanzu ya fi gaba daya zub da jinin da aka yi lokacin mulkin Jonathan.
"Don haka sai ka yi wa kanka adalci. Addininmu addini ne na adalci.

"A lokacin mulkin Jonathan, lokacin da jinin bayin Allah ke matukar kwarara a masallatai, cocina, da hanyoyi, na ce da shi yai murabus saboda na fuskanci ba zai iya magance zub da jinin ba. Ba zai iya magance wa ba. Na ce da shi ka taimaka ka sauka a yanzu-yanzu saboda ba zaka iya magance kashe-kashen rayukan mutane ba.

"Dalilin da ya sa kenan na yi kiran ya yi murabus, sannan jaridun gwamnati da ba na gwamnati ba suka wallafa. Shin hakan zai faru a yanzu?

"A yanzu an zubar da wani jinin sakamakon sakaci, bacci, lalaci da ko-in-kula."

Yake cewa halayyar ko-in-kula itace, yayin da ake karkashe mutane a cikin kasa, shugaban kasa da gwamnoni sai su dinga zabar halartar bikukuwan aure.

"Babu wata tambaya dangane da halartar bikukuwan aure.

"Idan zan yi wa kaina adalci, kamar yadda na yi kira ga Jonathan kan ya sauka, kamata ya yi in yi kira ga Shugaban Kasa Buhari da shima ya sauka, kuma a nan take! Kuma jaridun gwamnati suma ya kamata su dauka, in akwai gaskiya.

"Duk lalacewar Jonathan, ya fi bin dimokuradiyya, kuma ya bai wa mutane 'yancin fadin albarka cin bakinsu; koda sunanshi ne. Kun sheda lokacin da ya ga akwai matsala, sai ya bada mulkin, yake cewa 'Bana son a zubda jini.

"Wannan mutumin (Jonathan) ne ya gina mana jami'o'i guda tara a Arewa tare da makarantun Almajirai sama da 150. Har wannan titin jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna. Ya yi abubuwa da yawa. Amma na tuhumeshi saboda jini. Jini shi ne abin da ya fi komi tsada a rayuwa.

"Babu abin da ban ce ba (a kan Jonathan). A tsige shi, ya sauka....

"Don haka a yanzu ina da zabi guda biyu. Idan ba zan iya gaya wa dan uwana abin da na gaya wa wannan mutumin ba, to ya kamata in hau jirgi daga Abuja zuwa ga Jonathan sannan in ce masa don Allah ka yafe min sukar da na ma a bainar jama'a.

"Gara in nemi gafararshi, ko kuma shima shugaban kasar in sokeshi. Daya daga cikin biyun nan, ba wani na cikon uku.

"Mun yi ta hakuri da wannan gwamnatin. Da wata ce wallahi da ta fi wannan.

"Mutane na mutuwa ko yaushe. Jiya an yi garkuwa da wani. Mutane na wahala, sannan ba wanda zai iya fada saboda sun mallaki makogoronmu, saboda basa son jin wanni abu mara dadi game da mutumin. Wannan Masallacin Tauhid ne. Ko wannan isasshiyar hujja ce da za a nuna wa mutane.

"Lokacin da mutane ke cewa Annabi Isah Allah ne, Allah sai ya saukar da ayah domin ya nuna masa da Allah ya so zai iya ma hallaka shi."

Malamin ya ce idan mutane suka daga darajar dan Adam zuwa wani mataki, ya kyauta a yi wa mutumin jawabi domin a nuna wa mutane cewar shi mutum ne.

"Buhari cike yake da kuskure. Cike da kuskure! Mutum ne shi kamar kowa. Sannan na rantse da Allah cewar akwai mutane da yawa a nan Arewa da zasu iya tabukawa fiye da shi!"
sarauniya,

No comments:

Post a Comment